HAJJ 2023: Za Mu Kammala Jigilar Maniyyata  Kamar Yadda Muka Tsara (NAHCON)

Wasu Alhazai masu tafiyan aikin hajji

Shugaban ofishin kula da harkokin alhazai da ke Madina Ibrahim Idris Mahmud ya shaida wa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa suna gudanar da ayyukansu na jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki kamar yadda suka tsara.

Alhaji Ibrahim Idris ya kara da cewa suna bin dukkan tsare-tsare da dokoki na tafiyar da lamura kamar yadda Saudiyya ta tanada da hakan ya basu damar cin nasara a ayyukan nasu.

Alhaji Ibrahim ya ce daga cikin tsare-tsare da Saudiyya ta fitar akwai samun shaidar shiga RAUDHA AL-SHARIFAH (makwancin fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W) saboda yana daga cikin wuraren da ko wani Maniyyaci ya ke so ya ga ya kai ziyara, da hakan ya sa hukumar Alhazai ta kasa NAHCON tanadi ma’aikata don gudanar da aikin.

Mahajjata na tsaye a wani sansanin alhazai domin shiga jirgin saman zuwa Saudiyya

Ya ce sun fuskanci kalubale ganin cewa abu ne da ake yi ta yanar gizo inda ya ce wani lokacin abun yakan dauke amma duk da haka sun yi kokari wajen samar wa Alhazai 300 ta wannan hanya.

Sauran kalubalen sun hada da korafi na alhazai wajen jinkirin ba su masauki da abinci inda ya yi bayani cewa wasu lokutan ana samun hakan ne daga wajen Alhazan kuma sun yi nasarar shawo kan matsalar.

Kawo yanzu maniyyata dubu sittin da biyu da dari tara da saba’in da biyar (62,975) ne su ke kasa mai tsarki.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

HAJJ 2023.mp3