Hadin Kan 'Yan Sanda Da Miyetti Allah Ya Haifar Da Nasara

Kwamishinan 'yan sandan jihar Adamawa CP Audu Madaki, ya bayyanar da cewar wasu masu garkuwa da jama'a, da kuma gungun 'yan shila da suka kama.

Kwamishinan wanda yace nasarar ta samu ne lokacin da rundunan 'yan sandan ke mika lambar yabo ga shugabanin kungiyar Miyetti Allah, dake taimakawa a yanzu wajen zakulo masu garkuwa da jama'a, da ke boyewa a daji.

Kwamishinan ya yaba da hadin kan da yan Miyetti Allah ke badawa a yanzu, da ta kai har wasu guda biyar masu garkuwa da jama'a tuba. Ya kara da cewa rundunan 'yan sandan zata cigaba da hada kai da kungiyoyin sa kai don cin nasarar wannan illar.

A bayanin sa kuma game da makomar wadanda suka tuban, yace za su tura wa Shelkwata kan waddan da suka tuba, da wadan da suka kama, don ta bada umarnin hukunci a kai.

Alhaji Aliyu Abare, shugaban kungiyar Miyetti Allah na shiyyar Arewa maso gabas, ya wakilci shugaban kungiyar ta kasa, don gode musu da hadin kan da suka bayar.

Yanzu haka dai wannan matsalar ta garkuwa da jama'a na neman durkusar da harkokin kasuwanci a wasu sassan Najeriya. Alhaji Ibrahim Muhammad 86, mataimakin shugaban kungiyar 'yan kasuwa ta Najeriya mai kula da jihohin arewa 19, yace dole a tashi tsaye kan wannan matsalar.

A saurari cikakken rahoton wakilin muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Hadin Kan 'Yan Sanda Da Miyetti Allah Ya Haifar Da Nasara