Rashin tsaro na kan gaba wajen matsalolin da ke kawo kuncin rayuwa baya ga ‘dan karen tsadar kayan masarufi a kasar.
A taron da zauren ya gudanar a Abuja matasa da ke da kwarewa wajen fannoni daban-daban da wasu shugabannin al’umma sun zauna a teburi daya inda su ka yi bani gishiri in ba ka manja kan rashin tsaro.
Masu jawabai sun duba tushen tabarbarewar tsaro a arewa maso yamma da ya samar da barayin daji, illar rashin adalci, shan miyagun kwayoyi, bazuwar makamai, aikin ‘yan sa kai da sauran su.
Abba Danmaraya matashi da ya zo daga Kano wanda ke da kwarin guiwa kan cewa hada kai da matasa ne zai kawo maslaha “in a ka cigaba da hada kai a ka cigaba da karatu a ka cigaba da jajircewa wajen cewa mutanen da su ka cancanta su a ka zaba, abubuwan da su ka ta’azzara za su samu saukin su”
Ita ma matashiyar ‘yar siyasa Zainab Buba Galadima ta karfafa cewa sai kowane bangare ya sauke nauyin da ke kan sa kafin samun saukin rashin tsaro da ke hana hatta noma da ke zama kashin bayan tattalin arzikin arewa.
Shugabar zauren CONNECT THE DOTS Halima Abdulra’uf ta ofishin Muryar Amurka da ke Abuja ta ce shaukin ba da gudunmawa don saita ‘yan uwanta matasa ya sa ta shirya taron “ matasan nan wadanda su ke da basirar kirkire-kirkire ne, me ya sa ba a shigowa a dama da su?”
Baya ga malaman addini irin tsohon ministan sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami, Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal na daga bakin da su ka halarta da karin haske kan yanda su ke daukar matakan yaki da barayin daji.
Hakanan su ma sun saurari shawarwarin yanda za a samu bakin zare daga basirar matasa.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5