Hadarin Jirgin Sama Ya Kashe Mutane 19 a Sudan Ta Kudu

Hadarin Jirgin Sama a Sudan Ta Kudu

Hadarin Jirgin Sama a Sudan Ta Kudu

A sudan ta kudu mutane 19 sun halaka sakamakon hadarin jirgin sama a jiya lahadi, kamar yadda jami'an kasar suka fada.

Akwai akalla mutane 22 a cikin jirgin wand a ya tashi daga Juba babban birnin kasar kan hanyarsa zuwa birnin Yirol, lokacin da hadarin ya auku.

Wani dan kasar Italiya dake aiki da wata kungiyar agaji yana daga cikin wadanda ake ce sun tsallake rijiya da baya, kuma rahotanni suka ce raunukansa ba masu tsanani ainun bane,bayan da aka dauke shi zuwa Juba.

An sami hadurra a Sudan ta kudu cikin 'yan shekarun nan.

A halin da ake ciki kuma, a Kamaru mahukuntan kasar suka ce sun tura karin dakarun zuwa Bamenda sa'o'i masu yawa bayan da 'yan aware na kasar dauke da makamai suka hana shiga ko fita daga garin da galibin mazauna yankin suke magana da harshen turancin sarauniyar Ingila, dake arewa maso yammacin kasar, suna farwa motocin kiya-kiya da fasinjoji, kamar yadda Moki Edwin Kindzeka ya aiko mana daga Bamendan.