Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yankunan Somalia Biyar Suna Barazanar Ballewa Daga Kasar


Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed
Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed

Shugabannin yankunan kasar Somalia sun fada a jiya Asabar cewa zasu yanke duk wata alaka da gwamnatin tarayya, wani lamarin da ka iya haddasa koma baya ga yankin kuryar Afrika, bayan ya fito daga yakin shekaru ashirin.

A karshen wani babban taro mai muhimmanci a kudancin Kismayo dake gabar teku, shugabannin yankunan biyar da suka hada da Galmudug, Hirshabelle, Jubaland, Puntland and South West, sun zargi gwamnatin Somalia cewa ta gaza wurin karfafa tsaron kasa da kuma cika alkawarinta da ta yiwa yankunan kasar game da bin tsarin tarayya, bayan haka ta kuma watsi da yaki da kungiyar 'yan ta’addan Islama masu alaka da al-Qaida.

Jawabin bayan taron da shugabannin suka fitar yace, ganin cewa gwamnatin tarayyar ce ta haddasa tsamin dangantakar da su yankunan kasar, su kuma sun dace zasu dakatar da duk wata hulda da suke yi da gwamnatin har sai ta gyara kura kuranta.

Masu fashin baki sun bayyana damuwa cewa, rarraban kawuna da ake samu tsakanin yankunan da gwamnatin tarayyar, zai iya sake jefa kasar cikin wani rikicin siyasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG