Kocin kungiyar Newcastle united Rafael Benitez, ya bukaci ya cigaba da zama a kungiyar maimakon ya koma kungiyar Westham da aiki, sai dai kuma yace yana da bukatar shugaban kungiyar Newcastle, Mike Ashley ya bashi tabbacin cewar zai sake masa kudi na sayen ‘yan wasa a kakar wasan bana kafin ya amince da zaman sa a kulob din.
Benitez, dai yana bukatar da aba shi fam miliyan 100 domin ya sayo ‘yan wasa, haka kuma yana son a biya shi fam miliyan 6 a matsayin albashinsa duk shekara.
Kungiyar Juventus, tana da sha'awar dawo da Alvaro Morata, kulob din daga kungiyar Chelsea, Morata ya buga wasa a Juventus daga shekara 2014 zuwa 2016 a matsayin aro daga tsohuwar kungiyarsa ta Real Madrid kafin Chelsea ta saye shi.
Manchester united, tana gab da ta kammala sayen dan wasan baya na gefen hagu daga Juventus mai suna Alex Sandro, dan shekaru 27 da haihuwa akan kudi yuro miliyan €50 kimanin fam miliyan £43.7.
Arsenal ta ce zata sayar da danwasan tsakiyarta Aaron Ramsey, mai shekaru 27 a duniya in har bai sake sabunta kwantirakinsa a kungiyar ba.
Kungiyar Chelsea, ta kammala fidda sunayen ‘yan wasan da take da bukatar saye cikin ‘yan wasan harda dan wasan gaba na Manchester united, Anthony Martial, da kuma dan wasan tsakiya na mai suna Jean Michael Seri.
Your browser doesn’t support HTML5