Dan wasan tsakiyar Manchester United, Paul Pgoba, ya shaida wa ‘yan wasan kungiyar cewa yana so ya bar Old Trafford, da niyar komawa kungiyar Barcelona, amma idan Manchester United, tana bukatar ya cigaba da zama a kungiyar zata rika biyansa fam dubu 200 duk sati a matsayin albashi.
Manchester, dai tana zargin wakilin dan wasanne ke ingiza shi don ya koma Barcelona, har ila yau Manchester united, ta rasa sayen dan wasan Bayern Munich Jerome Boateng, sai dai Kocin kungiyar Jose Mourinho, ya shaida masa cewa yana godiya ga sha'awar da dan wasan ya nuna ta komowa kulob din amma hakan bai yuwu ba.
Mai tsaron raga na Kungiyar Athletico Bilbao, Kepa, wanda kungiyar Real tayi kwadayin sayensa akan kudi fam miliyan 17, yanzu haka yana dab da komawa kungiyar Chelsea, inda zai zamo mafi tsada a bangaren masu tsaron raga a duniyar wasanni bisa kudi har fam miliyan 71, dan wasan yanzu haka yana London domin kammala cinikin wanda zai maye masa gurbin Courtious, da yake shirin komawa kungiyar Real Madrid.
Real Madrid na iya maye gurbin Kovacic, da Thiago Alcantara, ko Miralem Pjanic. Darajar Alcantara zata iya kaiwa fan miliyan 54, yayin da dan wasan tsakiya na Juventus Pjanic, zai kai fam Miliyan £ 72m.
AC Milan, na tattaunawa akan dauko dan wasan Chelsea mai suna Tiemoue Bakayoko, mai shekaru 23, da haihuwa a matsyin aro. Crystal Palace da Fulham duka suna son sayen dan wasan gaba na Swansea City, dan kasar Ghana mai suna Jordan Ayew dan shekaru 26 a duniya.
Your browser doesn’t support HTML5