Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, José Mourinho, ya nuna rashin jin dadinsa ga hukumar gudanarwa ta Manchester, don ganin yadda batun sayen 'yan wasan yake tafiyar hawainiya a kungiyar,
Manchester United dai ta sayi 'yan wasa biyu kacal a shirye shiyenta na tunkarar kakar wasan bana na shekara ta 2017/18, wadda za'a fara a watan Agusta, mai kamawa.
'Yan wasan da Manchester ta saya sune Victory Lindelof, da kuma Romelu Lukaku, dan wasan gaba daga Everton, sai dai itama ta sayar da kaftin dinta Wayne Rooney, da kuma Adnan Januzaj.
Mourinho ya bukaci kungiyar da ta sake saya masa Karin 'yan wasa biyu kafin rufe hada hadar 'yan wasan kwallon kafa na bana.
A yanzu haka dai Manchester united, tana kokarin ganin ta sayo dan wasan tsakiya na gefe Ivan Pericis, daga kungiyar Inter Milan da kuma Nemanja Matic na kungiyar kwallon kafa na Chelsea.
Ita kuwa Chelsea ta amince da sayen dan wasan gaba na Real Madrid mai suna Alvaro Morata, akan zunzurutun kudi har fam miliyan £70.
Your browser doesn’t support HTML5