Hada - hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya

Lionel Messi

Kungiyar kwallon kafa ta Man City ta bayyana sha'awarta wajan neman shararren danwasan kwallon kafa na Barcelona mai suna Lionel Messi dan shekaru 29 da haihuwa.

Daga nan kuma sai kungiyar A C Milan wacce take neman dan wasan chelsea mai suna Juan Cuadrodo dan shekaru 28, da haihuwa.

Sai kuma kungiyar chelsea da tace bazata karbi kudin da suka gaza kudi yuro miliyan €30, ba ga duk mai bukatar dan wasan nata.

Ita kuwa Kungiyar Man Utd tana zawarcin dan wasan Juventus ne mai suna Leonardo Boncuci.

Chelsea kuma tana zawarcin dan wasan Napoli Kalidou Koulibaly dan shekaru 25 da haihuwa.

Shi kuwa dan wasan Kungiyar Leicester City Riyad mahrez, ya ce baya da ra'ayin zuwa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.

Daga karshe sai kungiyar Stoke city, wadda ta kammala sayen dan wasan kungiyar Al Ahly, ta kasar masar mai suna Ramadan Sobhi dan shekaru 19 da haihuwa akan kudi fan miliyan £5.