Gyaran Dokar Zabe: INEC Za Ta Baiwa ‘Yan Najeriya Mazauna Ketare Damar Yin Zabe

Mahmud Yakubu Shugaban INEC

Shugaban na INEC ya kara da cewa an shigar da shawarwarin cikin rahoton nazarin zaben Najeriya na 2023 mai shafi 524.

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa tana shirya gudanar da dimbin sauye-sauye a 2025 da zasu kai ga soke amfani da katin zabe na dindindin a lokacin zabubbuka, tare da baiwa ‘yan Najeriya mazauna ketare damar yin zabe.

A cewar INEC, an cimma wadannan shawarwari ne bayan kammala wani taro tsakanin shugabanta, Farfesa Mahmoud Yakubu da kwamishinonin zabe na jihohi a Abuja a jiya Alhamis.

INEC ta kara da cewa, nan bada jimawa ba za a gabatar da shawarwarin ga kwamitocin da suka dace a zaurukan majalisun tarayyar Najeriya guda 2.

Farfesa Yakubu ya bayyana cewa, mafi muhimmanci a cikin shawarwarin da suka bayar ita ce ta samun tabbacin kotu dangane da yadda za a gudanar da sakamakon zabe, ko dai a aike da dashi ta na’ura ko akasin hakan.

“Akwai kuma shawarwarin dake goyon bayan baiwa ‘yan Najeriya mazauna ketare damar yin zabe, da kuma tsatsaga hukumar sakamakon kafa kotun hukunta laifuffukan zabe da kuma wata hukumar ta daban da za ta kula da yiwa jam’iyyun siyasa rijista.

Shugaban na INEC ya kara da cewa an shigar da shawarwarin cikin rahoton nazarin zaben Najeriya na 2023 mai shafi 524.