Hukumomi suna can suna ci gaba kokarin gano musabbabin abin da ya yi sanadin faduwar wani jirgin saman kasar a karshen mako da ya gabata.
WASHINGTON D.C. —
A ranar Litinin kwararru masu iyo a karkashin ruwa na sojojin ruwan Indonesia suka fara neman wurin da na’urorin nadar bayanan jirgin saman fasinjan kasar, wanda ya fadi.
Hanyoyin sadarwar jirgin saman kamfanin Sriwajaya mai lamba SJ182 sun yanke ‘yan mintoci bayan tashinsa daga Jakarta zuwa Pontinak, babban birnin Lardin West Kalimanton da ke tsibirin Borneo, dauke da pasinjoji da ma’aikatan jirgin 62, ciki har da yara 10.
A jiya Lahadi masu aikin nema da ceto suka gano wurin da na’urorin biyu suke da ake kira black boxes da turanci bayan da suka gano wasu tarkace daga jirgin da ya fadi.