Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Neja Muazu Babangida Aliyu yace a kowace jiha akwai cibiyar da za'a ware domin kula da cutar.
Amma yace sun fi damuwa a jihar Neja kasancewa tana iyaka da jamhuriyar Benin. Yace suna da iyaka da kasashen waje. Lokacin da ake rikici sun lura cewa ana shogowa da makamai ta hanyar kogin kwara. Yace idan za'a iya shigowa da bindiga ana iya shigowa da gawar wanda ya mutu sabili da cutar. Dalili ke nan jihar ta fi kowace jiha damuwa.
Gwamna Aliyu yace suna son su fadakar da jama'a da shirin da ke kasa domin su tabbatar cewa an yi abun da ya kamata a yi . Amma kowace jiha, kowane gwamna ya san abun da zai yi sai dai wanda ya nuna halin ko in kula.
Gwamna Aliyu ya kara da yiwa jama'ar Neja gargadi akan cutar. Don Allah da an ce mutum ba lafiya a kira ma'aikatan asibiti domin a tabbatar da abun dake damunsa. Jama'a su kiyaye irin naman da zasu ci.
Kawo yanzu dai hukumomin kiwon lafiya a Najeriya sun tabbatar cewa wata likita da ta kula da wanda ya shigo kasar da cutar ita ma ta harbu da ita a Legas. Bugu da kari ana sanya idanu akan wasu mutane takwas domin tantance irin cutar dake tare da su. Yanzu dai gwamnatin Najeriya ta hana shigo da duk wata gawa daga kasar waje ba tare da tantance irin ciwon da ya kashe mutumin ba.
Yanzu dai cutar ta hallaka mutane 888 kamar yadda hukumar kiwon lafiya ta duniya ta sanar.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5