A yau Litinin gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 suka gana da sarakunan gargajiyar yankin a jihar Kaduna domin tattaunawa akan matsalolin dake addabar yankin.
Ganawar wani bangare ne na kokarin da kungiyar gwamnonin arewa ke yi na tattaunawa da muhimman masu ruwa da tsaki domin warware matsalolin dake damun yankin, musamman matsalar tsaron data ki ci taki cinyewa, da talauci da yara marasa zuwa makaranta da sauran kalubalen zamantakewar dake addabar yankin.
Ganawar wacce ta kasance karkashin jagorancin shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, kuma Gwamna Uba Sani ya karbi bakunci a fadarsa dake gidan Sir Kashim a Kaduna, ta samu halarcin gwamnonin jihohin Kaduna da Gombe da Zamfara da Nasarawa da Borno da Bauchi da Kwara da kuma Adamawa. haka kuma mahalarta taron sun kunshi mataimakan gwamnon daga sauran jihohin arewa.
Shima Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya halarci taron kuma ya yiwa gwamnonin jawabi akan kokarin da rundunar sojin Najeriya ke yi na shawo kan matsalolin ‘yan bindiga da ta’addanci da sauran kalubalen tsaron dake addabar yankin arewacin kasar.
Suma sarakunan gargajiyar da suka hada da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad da Shehun Borno, Umar El-Kanemi; da Sarkin Zazzau, Nuhu Bamalli; da Ohinoyi na kasar Ebira da Etsu Nupe, Yahaya Abubakar; da sarakunan Kazaure da Bauchi duk sun halarci taron.
A jawabansu na bude taro, Inuwa Yahaya da Uba Sani sun jaddada bukatar daukar matakan gaggawa na magance matsalolin tsaron da suka jima suna addabar yankin wadanda suka yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin arewacin Najeriya.