Duk da yake ba'a cika samun irin wannan lamari ba a Najeriya, Sarkunan da hakimai sun bayyana dalilan su na daukar wannan matakin.
'Yan Najeriya sun dade suna fama da matsalar rashin tsaro, halin kunci, fatara da rashin samun ci gaba a wasu wurare, kuma duka suna taka muhimmiyar rawa wajen wasu matakai da 'yan kasar ke dauka ga rayukan su.
Wasu daga cikin iyayen al'umman da suka yi murabus din, sun hada da Uban doman Gobir, Katukan Gobir, Mai garin Taka-tsaba, da sauransu, sun bayyana dalilan su na daukar matakin ne saboda koma baya da yankin ke fuskanta, da matsalar rashin tsaro, kuma sun karkata wilayar su zuwa ga sanata mai wakiltar su Ibrahim Lamido saboda a cewar su yana da zimmar fitar da su daga kangin rayuwa da suke ciki.
Ma'aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu da jihar Sakkwato ta ki cewa komai akan lamarin, amma shugaban karamar hukumar Sabon birni, Ayuba Hashimu yace, wasu daga cikin mutanen da suka ce sun ajiye sarautun su, sun dawo daga baya sun warware wannan magana kuma sun aminta da tsarin shugabanci da suke a kai tun farko.
Dandalin Mu Tattauna