SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da gwamnatin jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya ta kaddamar da wani kwamiti wanda zai bayar da shawarar yadda za a kafa rundunar samar da tsaron al'umma, kwanaki kalilan bayan gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da irin wannan rundunar.
'Yan Najeriya sun sha kokawa akan yadda matsalar rashin tsaro ke addabar yankunansu tsawon shekaru da dama, duk da matakan da mahukunta ke cewa suna dauka.
Yanzu wani mataki mai iya karfafa gwiwa da gwamanatocin arewa suka soma dauka shi ne na kafa rundunar samar da tsaro ga al'umma, kamar wadda gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar a makon jiya.
Gwamantin jihar Sakkwato ta biyo sawun jihar Katsina inda ta kaddamar da kwamiti da zai bayar da shawara akan yadda za a samar da rundunar tsaron al'umma.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu Sokoto, ya ce wannan wata matsaya ce da gwamnonin jihohin da matsalar rashin tsaro ta fi shafuwa suka cimma ta yin amafani da al'ummomin jihohinsu don samar da tsaron jama'a kuma sun sha alwashin aiwatar da shirin da gaske.
Wannan lamarin dai masana lamurran tsaro na ganin wani kyakkyawan yunkuri ne wanda ke iya karfafa gwiwar jami'an tsaro wadanda suma sun soma nuna bajinta a wasu wurare, kamar yadda suka hallaka 'yan bindiga masu yawa makon jiya a tsakanin jihohin Zamfara da Kebbi.
Dr. Yahuza Getso masanin tsaro a Najeriya ya ce kuma wannan ya zamo wani kalubale ga jami'an tsaron Najeriya na kara jajircewa duk da yake suna yin aiki cikin mawuyacin yanayi.
Baya ga jihar Katsina da ta kaddamar da rundunar da jihar Sakkwato da ta kaddamar da kwamitin samar da rundunar, jihar Zamfara ma ta yi nisa ga shirye shiryen yin hakan.
Saboda haka acewar masanin tsaro dole ne jami'an da aka dauka aikin da ma su kansu gwamnatocin su rika aiki tare da tuntubar juna domin sanin yanayin da ake ciki a ko'ina.
Wannan lamarin dai a iya cewa yazo lokacin da jama'a ke bukatar sa, musamman duba da kalaman shugaban kwamitin Kanar Garba Moyi Isa mai ritaya.
Wannan matakin dai da yawa daga cikin al'ummomin da ke yankunan da abin ya shafa na fatan ganin an dauka kuma ana yi da gaske sannan kuma an samu nasarar samar da tsaron.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5