Da yake zantawa da Muryar Amurka a Kano bayan taron Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yace sun tattauna ne akan hadin kai tsakanin majalisun tarayya da na jihohi.
Kazalika sun bukaci hadin kai tsakanin gwamnatocin jihohi da gwamnatin tarayya akan yadda za'a samo tsari mai kyau wanda zai tabbatar da samun zabe mai inganci da zai kara akan zaben shekarar 2015.
Gwamnan Tambuwal har wa yau yayi karin haske kan abubuwan da suka tattauna. Yace akwai batun yin anfani da naurorin zamani a zabukan kasar har su zama doka. Abu na biyu shi ne yadda za'a kyautata lokutan zabe domin a ba kutuna dama su kare duk kararrakin zabe dake gabansu kafin a rantsar da wanda ya ci. Abu na uku shi ne yiwuwar samun 'yan takara da basu da jam'iyya, wato masu zaman kansu.
Shi ko shugaban kwamitin lamuran hukumar zabe ta kasa wato INEC a majalisar dattawan Najeriya Sanata Abubakar Kyari wanda ya wakilci shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki yace yanzu ma a majalisar sun gabatar da kudurin kawo gyara a lamuran zabe. Yace lokacin zaben Kogi da dan takararsu ya rasu an samu matsala. Lokacin da abun ya faru babu dokar da ta tanadi abun da yakamata a yi. Yanzu suna neman a gyara da wasu dokokin da suka shafi zabe.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5