Gwamnoni Biyar Masu Neman Adalci

Gwamnan Jigawa Sule Lamido

Wasu gwamnonin jam'iyyar PDP su biyar sun ce babu ja ba komawa da baya saisun ga an yi adalci ba wai a jam'iyyarsu ba kadai har kasar ma gaba daya.
Gwamnonin PDP su biyar da suka yi suna wurin neman gyara a jam'iyyarsu wato Wamako na Sokoto, Aliyu na Neja, Lamido na Jigawa, Kwankwaso na Kano da Nyako na Adamawa sun ce babu gudu babu ja da baya sai sun ga an yi adalci a jam'iyyarsu da kasar gaba daya.

Gwamnonin sun ce muddin ba'a fitar da son rai ba to kasar zata koma gidan jiya.
Sun ce yawan tattaunawa da suke yi da tsoffin shugabannin kasar da wasu manyan mutane da wasu amintattu domin su sa kasar kan turba ta gari ne.

Gwamna Lamido na jihar Jigawa ya ce abun da suke yi shi ne mataki na biyu da kasar ta shiga.Ya ce matakin farko shi ne tabbatar da Najeriya. To an samu wannan. Najeriya ta tabbata. Mulki yanzu ba wai sai Bahaushe ko Bafullatani ba. A'a karamar kabila ma irin ta shugaba Jonathan na iya yi. Alamar cewa Najeriya ta gyaru shi ne ganin yadda karamar kabila ta samu shugabancin kasar. In ji Lamido zango na biyu shi ne ya fi wuya. A zango na biyu ana neman maganin ciwo wato ruwa, wuta, ilimi, zaman lafiya, hanyar mota da dai sauransu. Ya ce shin ko PDP ta shirya ta tanadi wadannan magunguna! Kamata yayi yanzu a samu gwmnati mai bin doka da oda da kuma tabbatar da doka da oda.

Ladan Ibrahim Ayawa nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnoni Biyar Masu Neman Adalci - 3:15