ABUJA, NIGERIA - Gwamnatin tarayyya ta bayyana cewa ta dakatar da shirin tallafin N-Power har sai yadda hali ya yi. A Gwamnatin tsohon Shugaban kasa Mohammadu Buhari ne a kirkiro da shirin a shekara ta 2016, wanda aka sa shi a karkashin shirin inganta rayuwar al'umma wato NSIP, wanda kuma ya kamata a yi amfani da shi wajen bunkasa rayuwar marasa galihu da matasa wadanda ba su da ayyukan yi.
Ita kuwa sabuwar Ministar jinkai da inganta rayuwa, Betta Edu ta yi zargin cewa akwai wani rashin gaskiya da aka gano wajen aiwatar da shirin.
Kamaludeen Kabir, mai magana da yawun wannan sashen na NSIP, ya ce wannan shiri na N-Power ba wai an soke ba ne saidai korafe-korafe aka samu daga wurin wadanda suke cin moriyar shirin inda wasu suka ce sun kwashi watanni takwas ko tara ko fiye da haka ba a biya su ba. Sannan akwai wadanda aka horar da su har an yaye su da jimawa amma ba a biya su ba balle su kama sana'a. Kamaludeen ya ce saboda haka ne Gwamnati ta dakatar da shirin na wucin gadi.
Kamaludeen ya ce ana so a gano halin da wadanda aka yaye su a shirin farko su ke ciki - wanda ake kira Batch 'A' da kuma yan Batch 'B' - kuma ba a biya su kudaden da ya kamata a ba su ba, saboda haka ana so a tuhumi shugabannin gudanar da shirin wato 'Consultants’, domin a gano inda kudaden suka makale.
Kamaludeen ya ce za a kara yawan wadanda za su ci gajiyar shirin daga miliyan daya zuwa miliyan biyar. Kuma za a tabbatar cewa ana da cikakken bayanin wadanda suka samu nasarar shiga shirin da adireshin inda suke da lambobin wayarsu da na danginsu, saboda idan ana so a same su, ba zai zama da wahala ba. Ma'aikatar ta ce bincike ya nuna cewa wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin sun yi batan dabo domin ba a same su inda aka rubuta cewa a can suke ba.
Amma ga Mohammed Aliyu, wani wanda yake cikin wadanda su ka amfana da wannan tsari na N-Power, ya bayyana ra'ayinsa a game da dakatar da shirin yana cewa kasa tana cikin wani hali na rashi, saboda haka wannan lokaci da aka dakatar da shirin bai yi ba. Mohammaed ya ce yana cikin wadanda suka mori shirin saboda yana samun ‘yan kudade na biyan bukatunsa na yau da kullum. Ya kuma kara da cewa dalilan da aka bayar na dakatar da shirin yana da kyau amma yana rokon a gaggauta kamalawa domin a maido da shirin.
Mai magana da yawun shirin, Kamaludeen Kabir ya tabbatar da cewa ana so ne a inganta tsarin domin a ci gaba da tallafa wa marasa galihu da kuma matasa.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5