Umarni dabam-daban da gwamnatocin kasashe suka dinga ba jama'a da su zauna a gidajensu kuma su guji shiga wuraren cunkoson jama’a na shafar rayuwar miliyoyin al’umma a fadin duniya, a yayin da hukumomin suke kokarin samar da ci gaba a yaki da annobar cutar Coronavirus.
Koriya ta kudu tana gudanar da kwakkwaran bincike da gwaje-gwajen mutanen da ke shigowa kasar daga wasu kasashe, don gudun yada kwayar cutar a cikin kasar, a dai-dai lokacin da aka samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar ainun.
China ma tana daukar irin wannan matakin. Ta bayyana samun sabbin wadanda suka kamu da cutar su 21, da duk suka danganci mutanen da suka shigo daga kasashen waje, in ban da mutum daya.
Kasashen biyu, sun sami gagarumar nasara a cikin makwanni biyu a baya-bayan nan, a yayin da sauran sassan duniya musamman kasashen Turai suka shige gaba da yawan masu cutar a fadin duniya.
Adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar Italiya, ya haura da fiye da mutane 3,000 a rana daya. Ya zuwa yau Talata, Italiya ta kasance kasa ta biyu da ke da mafi yawan masu dauke da cutar, kimanin linki biyu na adadin masu kamuwa da cutar a kasar Iran wacce ita ce ta uku a duniya.
Al’ummomi a fadin Amurka, sun dauki irin matakan da China, Koriya ta Kudu da Italiya suka dauka na takaita zirga-zirgar mutane da manyan taruka da suka wuce mutane 10, da kuma ba mutane umarnin su zauna a gida.