Rahotanni daga Gusau babban birnin jihar na nuna cewa cikin wadanda gwamnatin ke tuhuma har da wani mai shekaru 119 da ke cigaba da amsar albashi.
Indai binciken ya zama sahihi, a tsarin aikin gwamnati a Najeriya, ya zama wajibi ma'aikaci ya yi ritaya in ya cika shekaru 35 yana aiki ko kuma in ya cika shekaru 60 a duniya.
Dokar ta karawa wasu ajin ma'aikata kalilan da suka hada da alkalai shekaru biyar kafin su yi ritaya.
Mai taimakawa gwamnan jihar a fannin labaru da yanar gizo Zailani Bappah ya ce dubban sunaye aka gano na karbar albashi ta barauniyar hanya.
Kwamishinan kudi na jihar Rabiu Garba ya fito da batun binciken da nuna hatta mataimakin gwamnatin jihar da ke kan kujera Mahdi Ali Gusau ya samu neman bahasin ya na karbar albashi kashi biyu amma ya dau matakin kare kan sa.
Yawanci sabbin gwamnatoci na daukar irin wannan mataki na tantance yawan ma'aikata don rage makudan kudi da su ke tafiya wajen biyan albashi.
Ga dai rahoton Nasiru Adamu Elhikaya a kan batun:
Your browser doesn’t support HTML5