Gwamnatin Turkiya Na Cigaba da Kama Mutane

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan yana jawabi akan kokarin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Wata kafar yada labarai ta gwamnatin Turkiya tace yan sanda sun kai mamaya akan wasu kamfanoni 44 a Istanbul, yau Talata, wadanda ake zaton suna da hannu a yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba da aka yi a cikin watan jiya.


Kamfanin dillancin labaran na Anadolu tace an bada takardun samancin kama shugabannin kamfanoni 120 bisa zargin bada taimako ga shehun malamin nan Fetullah Gulen da yake zaune a nan Amurka.


Gwamnatin shugaba Racep Tayyib Erdowan tace Gulen shine ummul abaisan wannan yunkurin hambareta na ranar 15 ga watan Yuli, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 20


Hukumomi sun ce sama da mutane dubu 35 ne suke tsare a wani babban kame da aka yi ciki har da wasu jami’an sojin Turkiya da jami’an sassan shari’a da na ilimi.