Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Na Rokon Amurka Ta Mika Mata Mallam Gulen


Mallam Fethullah Gulen
Mallam Fethullah Gulen

Wata tawagar wakilan majalisar dokoki na Turkiyya suna nan Washington domin matsin lamba kan bukatar da kasar ta gabatarwa hukumomi a Washington, na ganin an mika mata tsohon Limamin nan Fethullah Gulen, wanda kasar take zarginsa da kitsa yunkurin juyin mulkin nan da bai sami nasara ba.

"Muna son ganin Amurka ta dauki muhimman matakai kan Fethullah Gulen, yayinda take nazarin bukatar ta tusa keyarsa, ta daure shi domin ta hana take takensa a Amurka," inji kamil Aydin, dan majalisa daga jam'iyyar MHP ya gayawa MA.
Shi da wasu wakilan majalisar dokokin kasar su uku sun gana da jami'an ma'aikatar shari'a ta Amurka jiya Litinin, kamin su zarce zuwa ma'aikatar tsaron gida.
Shugaban tawagar Taha Ozhan, ya gayawa MA cewa sun sami hadin kai a shawarwarinda suka gudanar a ma'aikatar shari'a. Taha shine shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje amajalisar dokokin kasar.
Ozhan, wanda dan jam'iyyar AKP ne wacce shi da shugaba Rajib Erdogan suka kafa ta, yayi gargadin cewa kin mutunta bukatar Turkiyya na mika mata Fethullah Gulen, zai yi mummunar illa ga dantakar kasar da Amurka da kuma yaki da ta'adanci.

XS
SM
MD
LG