Gwamnatin Turkiya Na Cigaba da Cafke 'Yan Jarida Tana Tsaresu

Shugaban Turkiya Recep Tayip Erdogan

Bayan yunkurin hambarar da gwamnatin Turkiya da ba yi nasara ba, ana cigaba da daukan mataki akan wadanda ake zaton suna da hannu a cikin harin.

Kimanin yan jarida 50 ne hukumomi ke bincikensu bisa tuhumar suna da nasaba da malamin Musuluncin nan Fethhullah Gulen wanda ake ganin shi ya shirya wannan yunkurin hambare gwamnati da ba yi tasiri ba a ranar 15 ga watan Yuli.

An bada sammancin tsare yan jarida da dama a farko farkon wannan mako.

Jaridar The New York Times ta bugo a jiya Talata cewa Gulen da ake zarginsa wanda yake zaune a Pennsylvania, yayi allah wadai da wannan hari kuma ya musunta masaniya a wannan hari. Kuma ya fito karara ya bayyana rashin amincewarsa da abinda ya kira mulkin kama karya da shugaba Racep Tayyib Erdowan ke yi, kuma yayi tir da yadda Turkiya take tafiya akan tsari mafi hadar na mutum daya ke cin karensa ba babbaka.

Yace Erdogan yayi barazanan zai janye gudunmuwan kasarsa a cikin rundunar hadin gwuiwa ta kasa da kasa masu yaki da kungiyar ISIS. Gulen yace bai kamata Amurka ta yarda da hakan ba.


Wani mai sharhi akan harkokin yau da kullum kuma farfesa a jami’ar Denver Jonathan Adelman ya shaidawa wakilin Muryar Amurka Vctor Beattie cewa sau tari yana dari dari da irin wadan nan kalamai, amma dai yana ganin akwai hikima ciki kalaman na Gulen.