Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta sauya wata matsaya da ta dauka wacce ta bukaci daliban kasashen waje da su canja makarantu ko su bar kasar idan jami’arsu za ta koyar da su darussa ne daga gida a dalilin barkewar annobar coronavirus.
An sanar da hukuncin ne a lokacin fara sauraron karar a wata kotun tarayya da ke Boston wacce Jami’ar Harvard da Cibiyar Fasaha ta Massachusetts suka shigar da ke kalubalantar matsayar gwamnatin.
Sanarwar ta samar da kwanciyar hankali ga dubban daliban kasashen waje da suke cikin hadarin a mayar da da su kasashensu.
Sannan daruruwan jami’o’in da ke ta fadi-tashin yadda za su bullowa karatun zangon farkon shigar lokacin hunturu bisa la’akkari da matsayar gwamnatin Trump sun Sami mafita.
Karkashin wannan tsari, daliban kasashen waje da ke zaune a nan Amurka ka iya fuskantar hadarin kasa yin karatunsu ta hanyar yanar gizo daga gida.
Hakan na nufin ba za a sabunta bizar daliban da za su yi karatu daga gida ba a wannan zangon karatu, ciki har da daliban jami’ar Havard.
Bincike ya nuna cewa, jami'o'i da kwaleji-kwaleji a Amurka, kan samu makudan kudaden shiga daga daliban wasu kasashe da ke zuwa kasar karatu.