GWAMNATIN TARAYYAR NIGERIA ZATA BIYA MARA SA AIKIN YI ALBASHIN NAIRA DUBU BIYAR.

  • Ladan Ayawa
Batun biyan alawus ga masu karamin karfi da sabuwar gwamnatin kasar tace zata fara

Mataimakin shugaban kasa farfesa Yomi Osinbanjo ya sanar da haka a garin Abeokuta ta jijhar Ogun a wajen wani toron da ya gabatar da kasida na inganta tattalin arzikin kasa.

Batun biyan alawus ga masu karamin karfi da sabuwar gwamnatin kasar tace zata fara biya da zaran ta gama nazari dai na daya daga cikin alkawuran da gwamnatin ta dauka a lokacin yakin neman zaben da ya gabata kuma kamar yadda mataimakin shugaban kasa Yomi Osinbanjo ya jaddada talauci yayi katutu a tsakanin yan Najeriya to kuma idan ana son a magance shi to wajibi ne gwamnati ta tallafawa marasa aikin yi da kuma masu zaman kashe wando domin su samu abinda zasu rika sakawa a bakin salati.

To anya kuwa gwamnati zata iya cika wannan alkawarin ganin dinbin matsalar rashin kudi da ake fuskanta abinda yasa ma a wasu jihohi ke kasa biyan albashin maaikata,

Mallam Sanusi Hassan masani harkokin tattalin arzikin kasa ne kuma tsohon maaikacin bankin UBA a Nigeria.

‘’Ai ina tabbatar maka abinda yafi dubu biyar idan gwamnatin tarayyar ta wannan kasar tayi niyyar ba talakawa domi tallafa musu domin rage talauci da radadin talauci da rashin babu da ake zama dashi a kasar nan zai yiwu, kuma hanyar guda daya ce kuma bata da wuya kuma kamar yadda shi mai girma shugaban kasa mai girma sir Muhammadu Buhari yasha fadi cewa idan ya samu aikin shugabancin Nigeria yan Nigeria sun bashi ALLAH ya bashi hanyar da zaibi ya samu kudin da za ayi aiki shine ya tottoshe kafofin da kudaden talakawa ke zurarewa wannan kafar koi ta ce kafar rashawa da cin hanci wadda tayi katutu a ko wane sako da bangaren gwamnatin Nigeria, yace idan ya toshe su to abinda ya samu daga wannan abin yace zaiyi anfani dasu wajen maganin talauci da kuma yiwa mutane aiki, musali yanzu akwai wata jihar duk sanin mu ana ciya da maaikatan gwamnatin jihar wadanda ke aiki a cikin gidan gwamnati a abinci rana kawai abindaake kashewa da abinda ake ba mutanen nan sama da shekara 16 nan da akayi ana mulkin farar hula wai naira miliya biyar ce kullun, a jihar a cikin sabbin gwamnoni da suka zo gwamnan yace ba zaiyi wannan ba aka dates wannan akwai wasu maaikatun gwamati wadanda sama da shekaru 10 ba maaikacin da yazo banda maigadi, wani gwamnan ya gano ana biyan naira miliyan 17 wanda ake cajin gwamnatin jihar kullun kuma mutum daya ne ke gadi wannan a cikin jiha daya Kenan kuma wannan abune kankani idan ka kwatanta da abinda ke faruewa a gwamnatin tarayya ALLAH kadai yasan abinda ke faruwa’’

Masana dai na ganin samar da kudin tallafi ba shine ,mafita ba ga talaucin da ake fuskanta sai dai samar da aikin ga jamaa musammam ma dai matasa sai dai a cewar Alhaji Garba Umar wani tsohon dan siyasa yace batun ace jama su dogara ga gwamnati wajen samar musu aikin yi yana da matukar wuya kuma kamata yayi ace kanfanoni masu zaman kansu da yan kasuwa suma su tallafa wajen samar da aikin yi a kasa.

‘’Abinda mukan manta wani lokaci shi samar da aiki a kasa bay a dogara bane kawai akan gwamnati bane bai yiyuwa gwamnatin kasa ko gwamnatin jiha tace ta wadatar da yayan jihar nan da aikin gwamnati kuma bai yiyuwa mu taallaka ga baki daya muce kowa sai yayi aikin gwamnati ko kayi makaranta ko baka yi ba dole masu hannu da shuni suma su shigo ayi wannan sune zasu bude masanaantu kanfanoni daban-daban da masanaantu daban-daban wadanda yake wadannan ai mutane za a dauka aiki mafi yawanci kuma wadanda za a dauka aikin nan matasa ne’’

Tuni dai gwamnati tace ta kudiri aniyar inganta hasken wutan lantarki da ya tabarbare a kasar abinda kuma tace zai bunkasa masanaantu su kuma su dauki jamaa aiki domin bunkasar tattalin arzikin kasar da kuma rage dogaro da man fetur.

Your browser doesn’t support HTML5

Albashin Naira 5,000 - 3'00"