Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Kara Kokarin Inganta Kiwon Lafiya

Likita ke duba matsayin lafiyar wata mata

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauki wani sabon mataki na tabbatar da cewa kowanne mutum ya sami kiwon lafiya nagari.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauki wani sabon mataki na tabbatar da cewa kowanne mutum ya sami kiwon lafiya nagari.

Gwamnati tayi haka ne ta wurin kaddamar da kwamitin mutum 12 na shugaban kasa a kan shirin lafiya na gaba daya karkashin jagorancin Mrs Fatima Bamidele, ta ma’aikatar lafiya.

Kwamitin zai shirya yadda aiki zai ci gaba a sashin lafiya, kuma an bashi tsawon wata hudu ya bada ruhotonsa.

A ranar kaddamar da wannan kwamiti, ministan lafiya, Prof. OnyebuchiChukwu yace, Mahimmin sakamakon da ake bukata daga wannan kwamiti shine hanyar da za’a bi domin tanada shirin lafiya ga dukan ‘yan Nigeriya a hanyar da zata iya iske kowa.

Sauran shirye shirye na bada lafiya suna karkashin shirin SURE-p da kuma shirin save one million live initiatives.