Kimanin kashi 40 na adadin mutane a duniya, yawancinsu wadanda ke zaune a kasashe matalauta, suna da hatsarin kamuwa da malariya. An sami kauda cutar a kasashe masu dumi a zamanin karni na 20. Amma malariya na da hatsari a yawancin kasashen Africa inda ta kashe fiye da mutane miliyan 300 a duniya, amma adadin wadanda ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar ya ragu zuwa mutuwar miliyan daya a shekara.
Kimanin kashi 90 na mutuwar ana tsammani zata kasance a kudancin Africa a kowanne sakan 30. Yawancin wadanda suka warke daga cutar suna fama da ciwon kwakwalwa ko kuma wahalar koyon karatu. Mata masu ciki da ‘ya’yan da basu isa haihuwa ba, suma suna fama da malariya, wanda ke kawo barin ciki da sauran cututtuka.
Kowacce shekara, mata masu ciki kimanin dubu goma, suna kamuwa da wannan cutar – malariya musamman, a yin cikinsu na haihuwar farko. Kariyar wannan cutar ya hada da amfani da rigar sauro mai magani. Ya kamata kowacce mace tana kwana cikin rigar sauro ta kuma rika shan magani (Sulfadaxine/pyrimethamine), kwaya uku sau biyu a lokacin ciki musamman makonni 16 na farkon ciki, da kuma sau uku lokacin ciki ga mata masu cutar sida.
Yana da muhimmanci mace mai ciki ta rika yin gwajin zazzabin cizon sauro kowanne lokaci har sai ta haihu.