Yanzu haka dai hukumar kula da sufuri da hanyoyin ruwa ta soma wayar da kan jama'a a kan wadannan sababin tsare-tsare a dukan yankunan da ke da hanyoyin ruwa.
Manajan Hukumar kula da sufuri ta hanyoyin ruwa mai kula da jihohin Sakkwato, Zamfara da Katsina Muhammad Bello Bala ya yi karin haske a kan wannan yunkurin lokacin da yake wayar da kan jama'a a Sakkwato a gulbin Rima, inda aka samu hadarin kwalekwale watan Agustan wannan shekara.
Bisa ga cewarshi, wannan sabon daftarin ya kunshi ka'idoji kamar yadda yake a kare hadarin mota.
Ya kuma bayyana wadansu daga cikin ka'idojin da suka hada da kakaba haraji ga duk mutumin da ya yi sanadin aukuwar hadari saboda son ransa. Haka ma ka'idojin sun hana lodi fiye da karfin abinda kwale kwale kan iya dauka, yayinda ake bukata a daidaita yawan lodin da zai dauka ta yadda nauyi ba zai rinjaya wani gefe akan wani ba. An kuma hana hawa kwalekwale daga karfe shida na yamma sai zuwa shida na safe.Har ila yau, dokar ta haramta shaye-shaye kafin a shiga kwalekwale,
Bayan haka kuma, hukumar bisa ga umurnin gwamnatin tarayya, zata samar da rigunan da ake sakawa idan za'a hau kwalekwale wadanda kan hana nutsewa cikin ruwa koda hadari ya auku.
Mazauna yankunan da ke da hanyoyin ruwa sun nuna gamsuwa da wannan tsarin sai dai sun jaddada bukatar aiwatar da tsarin yadda ya kamata ta yadda za'a ci gajiyar sa yadda aka tsara.
Tuni dai masana ke bayar da shawarwari yadda za'a a iya inganta sufurin ruwa ta yadda zai samu kulawa tamkar takwarorin sa na titi da sufurin sama.
A hirar shi da Muryar Amurka, Dokta Abdullahi Bello Tambuwal ya bayyana cewa, akwai bukatar samun kungiyoyin sa kai wadanda zasu taimaka wajen tabbatar da ana bin ka'idojin sufurin ruwa kamar yadda ake da wadanda ke kula da sufurin kasa.
Hadarin kwalekwale dai ya jima yana lakume rayukan 'yan Najeriya, domin ko watan da ya gabata na Agusta an samu aukwar hadarin kwalekwale hudu kasa ga mako daya, a jihohin Najeriya hudu da suka hada da Sakkwato, Bayelsa, Zamfara da Jigawa kuma an samu salwantar rayuka.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5