Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Ta Filato Zasu Kammala Gina Tashar Tekun Tudu

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta jaddada aniyarta na hadin gwuiwa da gwamnatin jihar Filato da kamfanin Duncan domin kammala aikin tashar tekun tudu da ake ginawa a Heipang cikin jihar

Ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi ya bayyana hakan yayinda yake rangadin gani da ido domin duba yadda aikin ke gudana.

Ministan ya fara ne da gabatar da roko ga gwamnatin jihar Filato da ta sa baki domin kamfanin Duncan ya janye karar da ya shigar saboda gwamnatin Jonah Jang ta dakatar da aikin a wancan lokacin tare da rushe mata wasu sassan gine ginen tashar.

Inji ministan yana son kwamitin dake farfado da aikin tashar ya tabbatar kafin watan shida na wannan shekarar an kammala aikin.

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong yace tashar zata inganta kudin shiga wa jiharsa tare da ba mutane musamman matasa ayyukan yi.

Shugaban hukumar hadahadar kasuwanci ta jiragen ruwa a Najeriya Hassan Bello yace tashar zata rage cunkoson da ake samu a tashar jirgin ruwa. Jirgin kasa zai kwaso kaya daga Legas ko Fatakwal ya kawo tashar hakan zai saukakawa mutane. Daga nan kuma kayan da za'a fitar waje a tashar za.a aika dasu ba sai an je tashar ruwa a Legas ko Fatakwal ba.

Daraktan kamfanin Duncan Godfrey Bawa yace yanzu sun kammala kashi hamsin na aikin tashar, kuma yace daga nan zuwa wata shida zasu kammala aikin.

Basaraken yankin Heipang yace zasu kare tashar kuma babu abun da zai sameta.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Ta Filato Zasu Kammala Gina Tashar Tekun Tudu - 3' 18"