A karo na biyu gwamnatin tarayyar Najeriya ta kebe Naira Biliyan 90, domin raba lamani ga gwamnatocin jihohin kasar 36 su sami sukunin aiwatar da kasafinsu na bana, rahotanni na cewa 7 daga cikin jihohin ne kawai suka cika sharrudan sabon lamanin makonnin biyu bayan gwamnatin ta amince a bada kudaden.
WASHINGTON, DC —
Sai dai masana tattailin arziki sun bayyana shakku akan yuwuwar cika sharrudan saboda tsaurin su.
Sharrudan dai sun hada da habaka hanyoyin haraji na cikin gida, da bayar da bayanan kashe kudade ga gwamnatin tarayya daga lokaci zuwa lokaci, takaita kashe kudaden gwamnati na rayuwar alatu, da kuma kafa hukumar bin diddigin kwangiloli da sauran ayyukan gwamnati da kuma amincewar majalisar dokoki ta jiha, duk wadannan sune daga cikin sharuddan da gwamnatin tarayya ta gindayawa kowacce jiha kafin ta samu sabon lamanin.
Ya zuwa yanzu dai jihohi bakwai ne suka iya cika wadancan sharruda daga cikin 36 na tarayyar Najeriya.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5