Yace ya kamata gwamnati ta sani cewa mutnen da suka koma wurarensu suna cikin wahala.
Shirin da gwamnatin tarayya ta yiwa mutanen arewa maso gabashin kasar da suka yi fama da rikicin Boko Haram ta fannin kudi da wasu taimako a fiddasu yanzu a rabawa mutane su fara rayuwa kamar yadda ake bukata.
Bishop Moses ya kira gwamnatocin jiha da na tarayya da su kafa wani kwamiti na musamman da zai kawo sulhu tsakanin jama'a.
Wakilan wadanda suka koma din su ma suna kokawa kan cewa tallafin da aka yi masu alkawari har yanzu bai kai wurinsu ba lamarin da ya sa har wasu sun fara kauracewa garuruwansu..
Mr Adamu Kamale dan majalisar wakilai dake wakiltar mazabar Madagali da Michika ya bayyana irin halin da mutane ke ciki a yankinsa. Yace mutane na cikin yunwa da tsananin kuncin rayuwa. Ya shawarci shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada abun da zai iya bada bisa ga alkawarin da ya yi.
Cikin watanni takwas zuwa tara da mutane suka koma babu abun da gwamnati ta yi.
To saidai gwamnatin Najeriya tace bata mance da halin da mutanen ke ciki ba. Hadimin shugaban kasa ta fuskar tsare- tsare ya bayyana irin tallafin da gwamnati ke bayarwa yanzu. Gwamnati na shirin tura 'yansanda da hukumomin tsaro zuwa arewa maso gabas domin kula da wadanda suka koma garuruwansu da kauyuka.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5