Hakan na zuwa sakamakon mawuyacin halin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fuskanta sanadiyar tsadar farashin kayan masarufi da abinci da kuma ci gaba da faduwar darajar Naira.
A da akwai ‘yan Najeriya kimanin miliyan 3 dake cin gajiyar shirin, yanzu gwamnatin tarayya ta kara magidanta milyan 12 da zasu ci gajiyar shirin rabon tallafin kudaden, sakamakon tashin gwauron zabbin da rayuwa tayi, inda adadin magidantan zai koma milyan 15.
Ministan Kudi da Bunkasar Tattalin Arzikin Najeriya, Wale Edun, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron nazarin manufofin ma’aikatar da ya gudana a Larabar nan, 21 ga watan Fabrairun da muke ciki, a birnin Uyo, na jihar Akwa Ibom.
Ministan ya kara da cewa Kwamitin Shugaban Kasa akan shirin tallafawa al’umma na daf da ganawa da Shugaba Bola Tinubu tare da bashi shawara akan sake farfado da shirin bada tallafin kudade kai tsaye ga ‘yan Najeriya mafi talauci da tsananin bukata.
“Muna sane da cewar akwai kimanin mutane miliyan 3 dake cin gajiyar shirin a halin yanzu, amma duba da yadda al’amura suka tsawwala ana hasashen akwai kimanin wasu mutanen kimanin milyan 12, da zasu iya shiga cikin shirin.”
A cewar Ministan, manufar fadada shirin itace kawai ga karin mutanen dake fama da kunchin rayuwa tare bada kudade kai tsaye ga wadanda ke matukar bukatarsu, domin basu damar zaben abinda suka fifita daga cikin bukatun da kuma yaye musu talauci.
Ya kara da cewar manufar shaidawa shugaban kasar game da abinda kwamitin ya zartar gabanin gabatar da rahoton karshe shine jawo hankalinsa game da wannan ci gaban, inda yace za’a yi amfani da fasaha wajen tabbatar da shirin ya gudana cikin sauke kuma a bayyane, inda za’a kaucewa hanyar ci da karfi da bata lokaci.