Daukan matakin dakatar da aiwatar da dokar hana kiwon, ya biyo bayan ziyarar kwamitin shiga tsakani ne da gwamnatin kasar ta kafa bisa jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, inda kwamitin ke ziyartar jihohin da aka samu tashe tashen hankula a tsakanin makiyaya da manoma
Kwamitin da ya kunshi gwamnoni tara da wasu manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki,na duba dalilan tashe tashen hankulan da ake samu da kuma hanyoyin magance su,kana kuma da yin nazari game da dokokin hana kiwo da wasu jihohi suka kafa.
To sai dai kuma da yake karin haske game da matakin da gwamnatin jihar Taraba ta dauka kan wannan doka a yanzu,babban mai shigar da kara,kuma kwamishinan harkokin sharia na jihar , Mr. Yusufu Akirikwen ya musanta rahotanin cewa gwamnatin jihar ta janye wannan doka,kwamishinan yace dokar na nan daram, to amma dakatarwa aka yi,domin yin gyaran fuska ga wasu sassan dokar.
Tun farko ma dai dokar ta jawo cece-kuce da kuma martani mai gautsi,musamman daga kungiyoyin Fulani makiyaya.To ko wane gyara dama suke bukata a yi? Sahabi Mahmud Tukur,shine shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah a jihar,ya bayyana inda suke bukatar gyaran.
Masana harkar sharia da kuma dokoki,na ganin akwai bukatar 'yan majalisu musamman ma na jihohi da su kiyaye irin kudurorin doka da gwamnoni kan kai gabansu,don kaucewa kitso akan kwarkwata. Barrister Idris Ibrahim Jalo,na cikin shugabanin kungiyar lauyoyin Najeriya,reshen jihar Taraba shi ma ya ba da shawara haka
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz domin karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5
.