Gwamnatin Syria suka sami nasarar zagaye birnin Aleppo na kasar, akalla mutane dubu 300 zasu shiga mawuyacin hali mai tsanani saboda ba za’a iya kai musu agajin tallafi kamar abinci da sauransu ba.
WASHINGTON DC —
A cikin bayanin da ta bayar a yau Talata, Majalisar-Dinkin-Duniya tace yanzu haka ma farmakin da sojan gwamnatin ke kaiwa ya janyo tsinkewar hanyoyin dake zuwa garin daga bangaren Bab al Salam dake wajajen kan iyakar Syria da Turkiyya.
Rahoton yace duk wata hobbasa da aka yi na dada katse hanyoyin ba abinda zai janyo illa tilastawa mutane tsakanin dubu 100 zuwa dubu 150 gudu, su bar Aleppo.
Hukumar Samarda Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace a kowace rana tana bada abinci ga mutane dubu 21 da suka gudo daga can Aleppo zuwa garin A’zaz dake kudu da kan iyakar Turkiyya.