Gwamnatin Siriya Zata Yi Kiran A Tsagaita Wuta

Qadri Jamil, mataimakin Firayim Ministan Syria mai kula da harkokin tattalin arziki a lokacin da yake wani dakin tattaunawa da manema labarai a birnin Moscow, Agusta 21, 2012.

Gwamnatin Syria tace zatayi kira a tsagaita wuta a wata tattaunawar zaman lafiya da MDD ta shirya, domin kawo karshen yakin basasar kasar.
Mataimakin Firayim Minista Qadri Jamil, shine ya gayawa jaridar Guardian cewa yakin ya tsaya a waje daya cak, yana mai cewa gwamnati da masu tawaye, duk basu da karfin cin galabar juna.

Ya gayawa jiridar ta kasar Britania cewa gwamnatin Syrian zata bada shawarar kawo karshen barin wasu kasashen ketare suna saka baki, da kuma shawarar fara gina tsarin siyasa na zaman lafiya, a tattaunawar da za’a yi a birnin Geneva, wanda aka dade da dakatar da shi.

Kasar Amurka da Rasha sun share watanni suna kokarin hade kan gwamnatin Syria da dakarun Tawaye a abinda aka kira “Geneva Two talks.”

A karon farko na wannan tattaunawa, ba’a cimma komai ba, saboda babu wanda ya wakilci duka sassan biyu. Masu adawan na Syria da kawunansu a rabe yake, sun ki hallartar tattaunawar wai har sai shugaba Bashar al-Assad yayi murabus.

Yunkurin kasa da kasa wajen kawo masalaha irin ta siyasa a rigingimu ya farfado bayan dai-daituwa da Amurka ta cimma da Rasha, akan Mr. Assad ya rabu da makamansa masu guba.

Kafin a yanke wannan shawara, Amurka tayi barazanar kai hare-haren soji domin ladabtar da gwamnatin Syria, saboda ance tayi amfani da makamai masu guba da suka kashe daruruwan mutane a wata unguwa dake kusa da birnin Damascus, wanda ke karkashin ikon masu tawaye a watan da ya wuce.