Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace a shirye gwamnatin shugaba Obama take ta taimaka iyaka iyawa wajen ganin Najeriya ta gudanar da zaben da zai zama karbabbe. Clinton ta bayyana haka ne jiya Alhamis a Washington bayan ganawarta da ministan harkokin kasashen ketare na Najeriya Henry Odein Ajumogobia.
Tace tattauwarsu ta bada karfi kan shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisa a watan janairu. Clinton ta bayyana kwarin guiwa kan shirye shiryen da aka yi kawo yanzu, yayinda ta yabawa burin shugaba Goodluck Jonathan na ganin an gudanar da zabe mai sahihanci, da kuma kafa sabuwar hukumar zabe. Ajumogobia yace Najeriya ta lashi takobin gudanar da zabe da zai zama karbabbe.
Bukatar yiwa tsarin zaben Najeriya garambawul ta bayyana a fili bayan zaben shekara ta dubu biyu da bakwai da kungiyoyin kare hakin bil’adama da kuma masu sa ido na kasa da kasa suka kushewa bisa hujjar cewa an tafka magudi da kuma tursasawa jama’a lokacin kamfe.