An tsige Shugabar Hukumar kula da hada-hadar hannayen jarin Nijeriya bayan an zarge ta da da laifin al’undahana da kuma rashin iya aiki.
Wani mai magana da yawun hukumar y ace an kori Darakta-Janar Ndi Okereke-Onyuike da yammacin Laraba da kuma babban shugaban hukumar da sauran mambobin hukumar gudanarwar hukumar.
Hukumar t ace an yi hakan ne don a gamsar da jama’a saboda yawan koke-koke game da rashin tafi da al’amura yadda su ka kamata a hukumar, da kuma matsalar shugabanci da kararraki da dama da hukumar ke fuskanta.
Ada dai sai a watan Nuwamba Okereke za ta yi ritaya.
A yanzu dai an nada Mr. Emmanuel Ikazoboh, wanda tsohon babban manaja ne a kamfanin hada-hadar kudi na Deloitte da ke Yammaci da Tsakiyar Afirka, a matsayin sabon shugaban hukumar na wucin gadi