Gwamnatin Somaliya ta aiwatar da hukuncin kisa akan wani tsohon dan jarida da aka zarga da taimakawa kungiyar Al Shabab, wajen kisan wasu ‘yan jarida su biyar a Mogadishu a tsakanin shekara ta 2007 da 2011.
WASHINGTON, DC —
Jami’ai da wadanda suka shaida lamarin sun ce an harbe Hassan Hanafi Haji a yau Litinin, a wata kwalejin horar da ‘yan sanda da ke Mogadishu.
A bara ne gwamnatin Somaliya ta nemi hukumomin Kenya su mika mata Hassan.
Mataimakin alkalin kotun soji da ta yankewa dan jaridar hukunci, Ahmed Hussein Mohammed, ya gayawa ‘yan jarida cewa an yiwa Hassan adalci a lokacin da ake yi mai shar’ia.
A cewar Mohammed, tun daga farkon shekarar 2015 ake mai shari’a, kuma ya amsa laifinsa, lamarin da ya sa kotun ta yanke mai hukuncin kisa.