A makon da ya gabata ne dai aka kai mummunan hari a Burkina Faso da yayi sanadiyyar asarar rayukan mutane da jikkata da dama awani katafaren Otal mai suna Splendid da ke Ouagadougou, babban birnin kasar.
WASHINGTON DC —
Burkina Fasa ta bada hutun kwanaki 3 a duk fadin kasar na makokin mutane 29 da suka mutu ‘yan kasashe 18 a mummunan harin da aka kai a wani babban Otal mai suna Splendid da ke babban birnin kasar.
Wadanda suka mutu a harin sun hada da wasu ‘yan kasar Canada guda 6, da ‘yan Faransa guda 2, da ‘yan Siwizilan guda 2 da kuma wani Ba’amurke guda 1. Sai kuma mutane da dama da suka jikkata.
Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore da ya fara mulkin kasar a watan da ya gabata yace, bayyana cewa, a karon farko kasar ta sami fadawa jerin munanan hare-haren da ake kaiwa a duniya.
Kungiyar ta’addar Al-Qaida Maghreb ne suka dau alhakin kai harin.