Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DIFLOMASIYYA: An Yi Musayar Sakin Fursunoni Tsakanin Iran Da Amurka


Ma'aikacin Jaridar Washinton Post Da Ke Tsare a Iran Kafin Sakinsa.
Ma'aikacin Jaridar Washinton Post Da Ke Tsare a Iran Kafin Sakinsa.

Karshe dai fursunonin da Amurka da Iran suka yi musanyarsu an sake su domin komawa ga iyalansu. wannan musanyar yafiyar fursunonin ta tabbata ne a jiya gaban manyan jakadun duniya.

Kasar Iran da Amurka sun yi wata musanya mai wahala ta sakin fursunonin juna a yau Asabar. Inda suka amince a gaban jami’an diflomasiyyar da suka taru a Vienna don karkare maganar takunkuman dake harde da Iran.

Cikin wadanda aka saki din har da Ba’amurken dan jaridar nan Jason Rezaian na Jaridar Washington Post, Sai wani Fasto, da wani sojan ruwa Ba’amurke dan asalin Iran. Gaba daya Amurkawan guda 5 aka saki.

Su kuma Amurka za su saki wasu Iraniyawa guda 7 da aka tsare kan zargin karya ka’idojin takunkuman karya tattalin arzikin Iran, da kuma wasu da ake tuhuma suma duk za a sake su.

Amurka ta bada sanarwar cewa ta yafewa dukkan wadanda ake zargin, kama tun daga kan wadanda ke tsare a gidan wakafi da kuma wadanda ake kan shari'arsu. An dai kwashe watanni 14 ana muzurai kafin kafin a cimma matsaya.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG