Gwamnatin Nijeriya Ta Bada Umurnin Bude Wasu Iyakokin Kasar

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwar bude iyakokinta na kasa guda hudu kuma a karshen watan Disamba za a bude sauran iyakokin kamar yadda Ministar kudi Zainab Ahmed ta bayyana a karshen wani taron majalisar ministocin kasar.

An dai rufe iyakokin Najeriya ne a watan Agusta na shekarar 2019, daya daga cikin dalilan gwamnati na rufe iyakokin sun hada da hana shigowa da shinkafa da zimmar bunkasa noman shinkafar cikin gida.

Sai dai Ministar Hajiya Zainab ta bayyana cewa za a ci gaba da aiwatar da dokar hana shigo da wasu kayayyakin, ciki kuwa har da shinkafa da sauransu. Iyakokin kasar da za a bude sun hada da Seme a kudu maso yammacin kasar, da iyakar Ilela a arewa maso yammacin kasar, da Maigatari da kuma Mfun.

Dr. Sani Gwarzo, babban sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya a ma’aikatar masana’antu da cinikayya, da saka hannun jari, ya shaidawa muryar Amurka cewa ci gaban dokar hana shigo da shinkafa kasar ya yi daidai domin a cewarsa, barin a shigo da shinkafa zai cutar da masana’antu da gonaki da manoman kasar.


Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, da jihar Katsina.