Gwamnatin Nijer Ta Dauki Sabbin Kwararrun Malaman Sakandare 2150

Wasu Malamai a Nijar

A ci gaba da neman hanyoyin farfado da sha’anin ilimi ke fuskanta a  jamhuriyar Nijer, gwamnatin kasar ta shigar da wasu malaman sakandare ‘yan kwantaragi sama da 2000 a sahun malaman dindindin ba tare da yin wata jarabawa ba.

Matakin da kungiyoyin malamai suka yaba da shi koda yake akwai sauran alkawuran da suke fatan ganin gwamnatin ta cika.

Kimanin malaman kwantaragi 2,150 da ke koyarwa a makarantun sakandare ne gwamnatin ta Nijer ta amince su shiga sahun cikakun ma’aikatanta, ba tare da rubuta wata jarabawa ba bayan da a bara wani bincike ya tabbatar da kwarewarsu akan aikin koyarwa.

Wannan wani yunkuri ne da gwamnatin ta Nijer tace ta na hangen inganta sha’anin karatun yara a karkashinsa bayan la’akari da koma bayan da tsarin kwantaragi ya haddasawa wannan fanni.

Tuni dai kungiyoyin malaman makaranta suka fara nuna farin ciki a game da wannan mataki koda yake ba za su yi gaggawar yanke hukunci ba, inji sakataren kungiyar malaman kwantaragi ta SYNACEB Cherif Issoufou, saboda tarin alkawuran dake tsakaninsu da bangaren mahukunta.

Kashi 80 daga cikin 100 na malaman dake koyarwa a makarantun gwamnatin Nijer duk ‘yan kwantaragi ne wadanda aka kyasta cewa yawansu ya kai 70000.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Nijer Ta Bayyana Shirin Daukan Sabbin Kwararrun Malaman Sakandare 2150