Gwamnatin Nijar Ta Janye Shirin Karbar Bashi Daga Bankin China

NIGER: SHUGABA MUHAMMADOU ISSOUFOU

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana janye wani shirin karbar bashin biliyan 1 na dalar Amurka daga EXIMBANK na kasar China sakamakon abinda ta kira rashin mutunta alkawalin da bangarorin biyu suka dauka a yarjejeniyar da suka sakawa hannu a shekarar 2013.

A ranar 30 ga watan Satumban 2013 ne hukumomin Nijar suka cimma wannan yarjejeniya da EXIMBANK a wani zaman da bangarorin suka yi a Beijing wacce a karkashinta bankin ya amince ya baiwa Nijar rancen miliyan 1000 na dalar Amurka da za a yi amfani da shi wajen aiwatar da wasu mahimman ayyukan ci gaban kasa a bisa sharadin ramka wadanan kudade ta hanyar danyen man da kasar ke hakowa a rijiyoyin Agadem.

Sai dai wata sanarwar da majalisar ministoci ta bayar a farkon watan nan na nuni cewa, Nijar ta canza ra’ayi saboda abinda ta kira rashin cika alkawali.

Sarkakiyar dake tattare da batun bashin EXIMBANK ya sa Firai Ministan Nijar Biirgi Raffini tuntubar kotun tsarin mulkin kasa a watan Agustan da ya shige domin ta haska fitila kan shirin gwamnati na janye kudirin karbar wannan rance. Kotun dai ta shaida mashi cewa, tilas ne a bi ta kan majalisar dokoki domin warware irin wannan yarjejeniya.

Faruwar wannan al’amari ya sa ‘yan Nijar jan hankulan hukumomi su yi takatsan-tsan a duk lokacin da kasar ke shirin cin bashi daga waje tare da tantance sahihancin hanyoyin da wadannan kudade zasu shiga..

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar ta fasa karbar bashin China-3:23"