Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da sayar da abinci a farashi mai rahusa a sassa daban-daban na kasar.
DAMAGARAM, NIJAR —
Hukumomin sun fito da wannan shiri ne don rage wa al'umma radadin tsadar rayuwar da ta tasa su a gaba wadda kuma yake da nasaba da karancin abinci da ake fuskanta a damunar bana.
Shi dai tsarin yana sayar da abincin ne ga talakawa banda ‘yan kasuwa yayin da aka dauki matakai, wanda kuma aka samu ‘yan farar hula a wajen don sa ido akan abinda ya je ya zo.
Tsarin sayarwar dai ko wane mutun gudu za a sayar mishi tiya biyar ta dawa, masara ko hatsi. Komai na tafiya sai dai dan jinkiri da aka fuskanta yayin da su kuma masu unguwanni suka koka da yadda aka yi burus da ake sayar ma ma'aikata alhali a cewar gwamnati ta ce na talakawa ne.
Saurari rahoto cikin sauti daga Tamar Abari:
Your browser doesn’t support HTML5