Ministan watsa labarun Nigeria Lai Muhammed shi ya kaddamar da yekuwar yaki da labarun karya tare da hadin gwuiwar jami’an tsaro na farin kaya.
Lai Muhammaed ya nemi hadin kan ‘yan jarida na kasa da kasa wurin cin nasarar yaki da wannan mummunan aiki dake yawan ruruta wutar rikici.
Yayinda yake jawabi Lai Muhammed y ace misalin labaran karya shi ne irin wanda jaridar Vanguard ta wallafa cewa wai hukumar zabe ta kasa, INEC, ta gano cewa hotunan yara dake kada kuri’a a lokacin zaben kananan hukumomi a Kano, amma karya ce aka yi. Yana cewa an yi haka ne domin a bata sunan hukumar.
Lai Muhammad ya kara da cewa a kokarin haddasa rigingimu da batanci a jihohin Plato da Binuwai tsakanin al’umma an dauko hotuna daga wasu kasashe ana yayata su ta shafukan sada zumunci na Facebook da WhatsApp da Twitter da gangan saboda a ruruta wutar fitina a kasa.
Bincike ya nuna cewa mutane miliyan 150 ne ke da wayoyin salula a kasar, kuma ta hanyar su ne ake yayata labarun karya dake zama kalubale ga mahukuntan kasar.
Wasu ‘yan majalisar kasa sun nuna goyon bayansu ga wanan yunkurin. Shehu Saleh Rijau dan majalisar wakilai daga jihar Niger y ace gaskiya yada labarin bogi na cikin abubuwan dake kawowa kasar matsala. A dauki mataki da zai kawo karshen yada labarum karya.
Shi ma dan majalisa Abdullahi Umar Faruk daga Gwandu jihar Kebbi y ace wannan abu ne da ya kamata a yi tuntuni kuma ‘yan jarida ya kamata a ce sun ba gwamnati gudummawa akan lamarin. Aikin ‘yan jarida ne su ilimantar da mutane da labarin da zai taimakesu ba wanda zai cutar dasu ba.
Kungiyar ‘yan jarida ta kasa ta ce a halin yanzu tana hada kai da mahukuntar kasar domin ganin an yi anfani da dokokin da ake dasu yanzu wajen yakar labaran bogi.
A saurari rahoton Medina Dauda
Your browser doesn’t support HTML5