Wannan dai na daga cikin muradun samar da bishiyoyi don cin ribar samun kudin shiga da kuma yaki da dumamar yanayi.
Hukumar, wadda ke aiki a jihohi 11 da ke fama da barazanar kwararowar hamada a arewacin Najeriya na gwagwarmayar ganin kowa ya dasa akalla bishiya daya, ya kuma kula da ita har ta kai ga samar da kariya da inuwa.
Shugaban hukumar Saleh Abubakar, ya ce an samo irin ne daga Afirka ta Kudu kuma duk wanda ya same shi zai rinka samun makudan kudi.
“Dabino zai tsiro cikin shekara 3 zuwa hudu. A kiyasin da muka yi, yanzu irin dabinon da za mu raba a kakar shuka da za mu shiga, za a samu naira biliyan 260 a shekara a matsayin kudin shiga. A saboda haka, wanda ya samu kamar 20 zai iya samun Naira miliyan daya a wata,” a cewar Abubakar.
Game da tsarin nan na dasa bishiyoyi da samun kudi daga kasashen ketare da ake kira Carbon Credit da turanci, Abubakar ya bukaci jama’a su kafa kungiyoyi don yin aiki da hukumar wajen samun kasafin. Ya kuma bada shawara cewa, “Ya kamata a hada kungiyoyi, a hada karfi da karfe ta yadda dukkanmu zamu fito mu yi aikin tare. Kuma kowa ya yi kokari ya yi lambu a cikin gidansa inda zai rika samun kayan miya, duba da yadda ake fuskantar matsin tattalin arziki,”
Gwamnatocin jihohi da kungiyoyi sukan kaddamar da aikin dashen bishiyoyi amma wasu lokutan ba sa samun kulawa bayan kammala bukin kaddamar da aikin.
Lamarin dausayin yankin arewa ya hada da kogunan da hamadar ke kadar da su, musamman a lokacin rani, kamar yadda Musa Bala Yakasai, ko-odinetan kungiyar Arewa Green Movement na kasa ya bayyana. Akwai wani abu da a ke kira River Bank da turanci, to shi kogin Hadeja Jama'are ya taho ne daga yankin da ya hada da tafkin Chadi, to ranar da hanyar ruwa daya ta toshe, samar da ita zai gagara. Dalilin da ya janyo janyewar ruwan Hadeja da Jama'are kenan. Don haka sai an yashe kogin na Hadeja Jama'are kafin ruwa ya gudana yadda ya dace, ta yadda manoma zasu samu gabar ruwa har tsirrai su fito.
Har yanzu ana ci gaba da sare bishiyoyi don samun itacen girki, duk da samun zabin hanyoyin makamashin girki masu rahusa.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5