AGADEZ, NIGER - A tsawon kwanaki uku masanan da kungiyoyin kasa da kasa da makiyayan sun soki irin son kan da suka ce kasashe masu galihu su ke nunawa a fannin sauyin yanayi, dake zaman musabbabin sauyin yanayi da kasashen suka tsinci kan su a ciki.
Masansan sun bayyana haka ne a wajen wani taro inda suka koka da irin halayen da kasashen ke nunawa wajen daukar matakin da zai rage illolin da sauyin yanayi ke haifarwa a kasashe marasa galihu irin na Sahel.
Taron na karon farko ya mayar da hankali ne kan hanyoyin da za’a bi don kaucewa irin illoli da asarar da sauyin yanayi ke haifar wa a yankin.
Mahalarta taron dai sun bukaci kudin diyya saboda irin asarar da suka tabka da ke haifar da wahalar bala’o’i da ake fuskanta a kasar kama daga ambaliyar ruwa, kwararowar hamada.
Makiyaya da suka halarci taron na ganin akwai bukatar a samar da shawarwari na bai daya wanda za a gabatarwa shugabannin yankin.
A karshe dai mahalarta taron sun fitar da wani dafatari domin jaddada mahinmancin yankin wajen zama mahinmin bangare inda ya kamata a karkata domin samun mafita kan sauyin yanayi dake addabar duniya.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna