Shugaban ya bayyana hakan ne a taron karawa juna sani kan ilimi na duniya mai taken "daukar nauyin hadin gwiwa a bangaren ilimi", wanda ya gudana a birnin Landan na kasar Burtaniya.
A cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran ma’aikatar ilimi ta Najeriya, Ben Goong ya fitar, shugaba Buhari, ya kara jaddada kokarin gwamnati na tabbatar da karin kaso 50 cikin 100 a kudadden da ake ware wa fannin ilimi a kasar a cikin shekaru biyu.
Haka kuma karin zai iya kai har zuwa kashi 100 bisa 100 nan da shekaru biyar wato daga shekarar 2021 zuwa 2025.
Buhari ya kuma lashi takobin yin aiki da jihohin kasar 36 hade da babban birnin tarayya Abuja, domin tabbatar da samun ci gaba, ta hanyar tabbatar da yin amfani da sama da kashi 20 cikin 100 na kasafin kudi da ake ware wa bangaren ilimi domin cimma nasarar a tsarin daidaituwar ilimi a fadin Najeriya.
Gwamnatin Najeriyar na kuma duba yiyuwar yin kari kan harajin ilimi da kaso 2 zuwa 3 cikin 100 domin kula da tsarin ilimin jami’o’in kasar tare da yin kari a asusun haraji da ake samu ta fuskar tattalin arziki wato CRF don tallafawa ilimin firamare da sakandare daga kaso 2 zuwa 4 cikin 100.
Shugaba Buhari ya kuma sha alwashin kawo karshen matsalar yara da ba sa zuwa makaranta ta hanyar tabbatar da samun ilimi ga yara miliyan 10 da ba sa makaranta a halin yanzu.
Ya kuma ce za'a bunkasa fannin koyar da sana’o’in hannu ga yan Najeriya, da kuma aiwatar da shirye-shirye kan ilimin bai ɗaya, ilimin yara mata, Ilimi na musamman, ilimi ga masu yawan shekaru da kuma shirye-shiryen makarantu na musamman wadanda za su ba da fifiko kan inganci da kima ga kammala karatun firamare da sakandare da dai suransu.