Gwamnatin Najeriya ta ce tana tattaunawa da kungiyar Boko Haram a kan yiwuwar tsagaita wuta, kuma wannan tattaunawar tayi nisa, kamar yadda ministan yada labarai Lai Mohammed ya bayyana a jiya Lahadi.
Wannan shine karon farko a cikin shekaru da gwamnatin ta fito ta bayyana cewa tana magana da Boko Haram kan shirin tsagaita wuta. Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fada a baya cewa a shirye take ta gudanar da shawarwari da mayakan sakan, amma bata bada wani karin bayani ba.
Ahalinda ake ciki kuma, sama da yan mata dari da mayakan Boko Haram suka sako, sun koma ga hannun iyayensu jiya Lahadi.
A cikin watan Faburariru ne mayakan sakan suka yi garkuwa da yan matan da suka sace su daga garin Dapchi.
Bayan an sako ‘yan matan a ranar Laraba da ta gabata da kuma takaitacciyar ganawa da ‘yan matan suka yi da iyayensu cikin yanayi na tausayi, ‘yan makarantar sun kwashe kwanaki uku suna Abuja babban birnin kasar, inda suka gana da shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari yayi alkawari a ranar Juma’a cewa, zai yi iya bakin kokakrinsa ya tabbatar da an sako yarinya daya da ta rage hannun ‘yan Boko Haram mai suna Leah Sharibu wacce itace kadai kirista, kuma taki ta canza addininta.