Gwamnatin Najeriya Ta kwashe Rukunin Farko Na ‘Yan Kasar Da Suka Gujewa Yakin Sudan.

Rukunin Farko Na 'Yan Najeriya Da Aka Dawo Da Su Daga Sudan

Gwamnatin Najeriya ta yi nasarar kwashe ‘yan Najeriya wadanda suka gujewa yakin Sudan. da suka hada da dalibai da iyalai masu kananan yara.

Hidimar kwashe mutanen wani bangare ne a kokarin gwamnatin Najeriya na tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasar a kasashen ketare, musamman kasar Sudan, inda a halin yanzu ake fama da rikici, tabarbarewar siyasa da tattalin arziki.

Jirgin ya taso ne daga Kasar masar inda ya isa filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya Abujan Najeriya, Jirgin farko ya sauka a Abuja ne da misalin karfe biyun dare bayan lokacin da aka tsara, amma an kai dukkan wadanda aka kwashe cikin koshin lafiya.

Rukunin Farko Na 'Yan Najeriya Da Aka Dawo Da Su Daga Sudan

A hirar ta da manema labarai, Miinistar harkokin jinkai, Sadiya Farouq tace, mutane 282 ne jirgin Air Peace ya yi jigilarsu, yayin da NAF ta kai mutane 96 da aka kwashe.

Farouq ta bayyana matukar jin dadinta da cewa duk wadanda aka kwashe sun dawo Najeriya ba tare da sun samu matsala ba, inda ta ce an yi aikin dawo da su gida ne ba tare da an samu asarar rai ba.

Rukunin Farko Na 'Yan Najeriya Da Aka Dawo Da Su Daga Sudan

Ta kuma kara da cewa, za a ba wa wadanda aka kwaso kayan alfarma, wadanda suka hada da alawus din sufuri na naira 100,000, katin kira na Naira 25,000 da kuma data kimanin 1.5 GB.

Jakadan Sudan a Najeriya, Mohamed Yousif, ya halarci filin jirgin domin tarbar mutanen da aka kwashe tare da nuna nadamar halin da ake ciki a Sudan tare da nuna jin dadinsa da cewa mutanen sun koma gida lafiya.

Dawowar 'Rukunin Farko Na Yan Najeriya Daga Sudan

Nasarar kwashe kashin farko na ‘yan Najeriya daga kasar Sudan ya samu yabo daga ‘yan Najeriya da dama, inda suka nuna jin dadinsu ga gwamnati kan tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasar a kasashen ketare.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, za ta ci gaba da ba da fifiko kan tsaro da jin dadin ‘yan kasar ta gida da waje.

Nasarar dawo da rukunin farko na 'yan Najeriya gida daga kasar Sudan, wata shaida ce da ke nuna yadda gwamnati ke kokarin tabbatar da tsaro da jin dadin 'yan kasar.

Ku Duba Wannan Ma An Fara Zargin Baki Da Goyon Bayan Dakarun RSF A Fadan Sudan

~Yusuf Aminu Yusuf~